logo

HAUSA

Kasar Sin za ta baiwa Palasdinwa taimakon jin kai na dala miliyan 1

2021-05-21 19:59:32 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai Jumma’ar nan cewa, kasarsa za ta samarwa Palasdinawa taimakon jin kai na gaggawa na tsabar kudi har dalar Amurka miliyan daya.

Zhao ya ce, haka kuma kasar Sin, za ta baiwa hukumar MDD mai kula da rage radadi da ayyukan kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu dake yankin Gabas ta Tsakiya gudummawar dala miliyan daya da alluran riga kafin COVID-19 dubu 200.

Tun da farko mai magana da yawun hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin (CIDCA) Tian Lin, ya samar cewa, kasar Sin za ta samarwa gwamnatin Palasdinawa taimakon jin kai, domin jinyar wadanda suka jikkata da sake tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu.

A jiya ne dai, kasar Sin ta kaddamar da shirin samar da taimakon jin kai. Yanzu haka dai, Isra’ila da Hamas, sun amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kasar Masar ta shiga tsakani, da nufin dakatar da fada da misalin karfe 2 na sanyin safiyar yau Jumma’a, agogon wurin, domin kawo karshen mummunan musayar wuta na tsawon kwanaki 11.

Ibrahim