logo

HAUSA

Gwamnatin Tsakiya Ta Kasar Sin Ta Ware Yuan Triliyan 1.63 Ga Tibet Cikin Shekaru 70 Da Suka Gabata

2021-05-22 16:23:34 CRI

Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta zuba jarin da jimilarsa ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 1.63, kimanin dalar Amurka biliyan 253 a yankin Tibet mai cin gashin kansa na kasar, cikin shekaru 70 da suka gabata, bayan da aka ‘yantar da yankin cikin lumana.

Sakataren kwamitin yankin Tibet mai cin gashin kansa na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wu Yingjie ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka shirya a yau Asabar ranar 22 ga wata, kan ci gaban zamantakewar al’ummar kasa da tattalin arzikin yankin Tibet mai cin gashin kansa, inda ya yi karin bayani da cewa, yankin mai cin gashin kansa na kudu maso yammacin kasar Sin, ya kuma karbi kudaden da jimilarsu ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 69.3 daga sauran gwamnatocin birane da larduna a shekarun baya-bayan nan.

A cewarsa, an zuba sama da kudin Sin RMB yuan biliyan 590 cikin ginin manyan ayyukan da suka yi matukar ingiza yankin ga samun ci gaban tattalin arziki, ciki har da babban titin da ke tsakanin birnin Chengdu na lardin Sichuan da birnin Lhasa na yankin Tibet mai cin gashin kansa da layin dogo da ke tsakanin birnin Xining na lardin Qinghai da birnin Lhasa na yankin Tibet mai cin gashin kansa.

Jami’in ya ci gaba da cewa, ana maraba da jarin waje a yankin na Tibet mai cin gashin kansa, kuma yankin zai ci gaba da dukufa wajen kyautata amfani da kudade, yana mai cewa, Tibet ya yi amfani da jarin waje da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 400. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha