logo

HAUSA

Shin 'Yan Majalisar Turai Za Su Yi Wa Kasar Sin Sharri Ne Kan Yarjejeniyar Zuba jari Ta Sin Da Turai?

2021-05-21 21:20:53 CRI

Majalisar Turai ta yi wa kasar Sin sharri bisa yarjejeniyar zuba jari ta kasashen Sin da Turai, a yunkurin ganin kasar Sin ta mika wuya. Sanin kowa ne cewa, yunkurin majalisar Turai rashin tunani ne.

A yammacin jiya ne, majalisar Turai ta zartas da wata shawara, inda ta bukaci kasar Sin ta soke takunkumin da ta sanya wa EU kafin a amince da yarjejeniyar zuba jari da Sin ta kulla da Turai. Akasarin ra’ayoyin jama’a na ganin cewa, matakin ya dakatar da wannan yarjejeniya, wadda Sin da Turai suka dauki shekaru 7 suna tattaunawa.

Matakin da majalisar Turai ta dauka ba shi da ma’ana, ta dauki matakin ne ba bisa sanin ya kamata ba. Me ya sa Sin ta sanya wa Turai takunkumi? Saboda Turai ta sanya wa daidaikun Sinawa da hukumomin Sin takunkumi bisa karyar da aka baza kan batun Xinjiang a watan Maris na bana. Ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, tare da saba dokokin kasa da kasa da muhimman ka’idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin ta mayar da martani ne kawai. Ta kiyaye moriyarta ne kawai. Don haka, matakin da ta dauka ya wajaba.

Yanzu majalisar Turai ta bukaci kasar Sin ta soke takunkumin, lamarin da ya yi kama da yadda kasar Sin ta ki mayar da martani yayin da aka bata sunanta. Bukatar majalisar Turai ba ta da ma’ana.

Wa zai kara damuwa idan ba a zartas da yarjejeniyar zuba jari ta Sin da Turai ba? Kamfanonin kasashen Turai ne! A cikin shekaru 20 da suka wuce, sun zuba kudin Euro biliyan 146 a kasar Sin, sun kuma ci riba da yawa. Yanzu babbar kasuwar kasar Sin mai yawan mutane biliyan 1.4, tana kara samun ci gaba, tare da kara bude kofa ga kasashen ketare. Yadda majalisar Turai ta dauki wannan mataki, tamkar kwace riba ne daga hannun kamfanonin Turai, tare da ba wa sauran kasashe ribar.

Bai dace a sanya siyasa kan yarjejeniyar zuba jari ta kasashen Sin da Turai ba. Majalisar Turai ta yanke wannan shawara ce ba bisa tunani ba, tabbas ba za ta yi nasara ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan