logo

HAUSA

Tibet ta kaddamar da ayyuka daban-daban don bikin cika shekaru 62 da yantar da miliyoyin bayi manoma

2021-03-28 17:35:36 cri

Yau Lahadi, ranar bikin tunawa da ‘yantar da miliyoyin bayi manoma na jihar Tibet ta kasar Sin. A safiyar ranar ta yau, mazauna birnin Lhasa sama da dubu daga kabilu daban daban da bangarori daban daban sun hallara a filin Fadar Potala don gudanar da bikin "Daga tutar kasa da rera taken kasa" don murnar cika shekaru 62 da ‘yantar da miliyoyin bayi manoma.

A wannan rana kuma, dakin tunawa daya kacal game da aikin kawar da tsarin bauta a kasar Sin, wato dakin tunawa da ‘yantar da miliyoyin bayi manoma na Tibet an bude shi a hukumance a wannan ranar, wanda ya jawo hankalin mutane masu yawa don ziyarta.

A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 1959, a karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, an gabatar da wani gagarumin garambawul na dimokiradiyya a jihar ta Tibet, inda aka rusa tsarin bauta da ya hada mulkin siyasa da addini. Hakan ya sa miliyoyin bayi manoma na Tibet sun zama shugabannin kasar da na al'umma, kamar sauran mutanen kabilu daban daban na kasar.

A cikin shekaru 62 da suka gabata, yawan GDPn jihar Tibet ya karu daga yuan miliyan 174 a shekarar 1959 zuwa yuan biliyan 190 a shekarar 2020, kana yawan kudin shigar da mazauna jihar suka samu ya tashi daga ba ko sisi zuwa yuan 21,744 a shekarar 2020, kuma matsakaicin yawan rayuwa ma ya karu daga shekaru 35.5 a shekarar 1959 zuwa shekaru 71.1 a yanzu haka. (Bilkisu)