logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kiwon lafiyar kasa da kasa

2021-05-20 11:33:38 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta sanar a yau Alhamis cewa: Bisa gayyatar Mario Draghi, firayim ministan kasar Italiya dake rike da shugabancin kungiyar G20, da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai Von Der Leyen suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kiwon lafiyar kasa da kasa ta hanyar bidiyo a Beijing a ranar 21 ga watan Mayu, inda kuma zai gabatar da muhimmin jawabi. (Bilkisu)