logo

HAUSA

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Kira Taron Manema Labarai Game Da Shirin Abokantaka Na Goyon Bayan Raya Afirka

2021-05-20 20:38:52 CRI

A yau ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta shirya wani taron manema labarai game da “Shirin abokantaka na goyon bayan raya Afirka”. A jawabinsa babban darektan sashen harkokin Afirka a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wu Peng ya bayyana cewa, a baya kasashen Sin da Afirka sun inganta tattaunawa da tuntubar juna game da “Shirin abokantaka na goyon bayan raya Afirka”.

A jiya ne dai, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, tare da kasashe Afirka, suka kaddamar da shirin, yayin taron manyan jami’ai na kwamitin sulhun MDD game da “Zaman lafiya da tsaro a Afirka: Bunkasa farfado da Afirka bayan annobar COVID-19, da magance tushen rikice-rikice”.

Wu Peng ya bayyana cewa, shirin ya kunshi shawarwari 23, da suka hada da, bayyana matsayi, da manufofi da matakan da kasar Sin ke dauka game da ci gaban Afirka, abin da ke kira yin ga kasashen duniya, da su karfafa dabarunsu na raya kasa da ma Afirka a fannin yaki da annobar COVID-19, da sake gina nahiyar bayan annobar, da cinikayya da zuba jari, da soke basussuka, da samar da abinci. Sauran sun hada da kawar da talauci, da tattalin arziki na zamani, da sauyin yanayi, raya masana’antu, da jin dadin jama’a, musamman a hada ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063, da shirin raya nahiyar na shekaru goma na farko tare, ta yadda nahiyar za ta samu ‘yanci da ci gaba mai dorewa nan da nan.

Wasu wakilai daga kasashen Afirka, sun yi karin haske game da shirin da kasashen Sin da Afirka suka gabatar, inda suka yi kira ga dukkan kasashen duniya, da su ba su goyon baya, ta yadda za su dauki matakan da suka dace don ci gaban nahiyar. Sun kuma bayyana kudirinsu na yin aiki tare da kasar Sin wajen ganin an aiwatar da shirin.

Ibrahim