logo

HAUSA

Mene Ne Amfanin Amurka A Rikicin Palasdinu Da Isra’ila

2021-05-17 21:18:06 CRI

A matsayinta na shugabar karba-karba na kwamitin sulhun MDD na watan Mayu, jiya kasar Sin ta jagoranci wata muhawarar gaggawa dangane da rikicin da ke faruwa tsakanin Palasdinu da Isra’ila, inda taron ya yi kira ga bangarorin 2 da su tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, ya kuma jaddada cewa, tilas ne kasashen duniya su dauki matakai cikin hanzari, musamman ma kasar Amurka, ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, ta yi adalci kan rikicin, tare da goyon bayan kwamitin sulhu da ya taka rawa wajen sassauta rikicin, da maido da amincewa da juna a tsakanin bangarorin 2 da daidaita rikicin a siyasance.

Me ya sa ake ambato Amurka yayin da ake maganar rikicin da ke tsakanin Palasdinu da Isra’ila? Saboda rikicin da ke kara tsananta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a halin yanzu, wanda ya fi muni tun bayan yakin zirin Gaza a shekarar 2014, wani mummunan sakamako ne da aka samu bayan da Amurka ta aiwatar da manufofi marasa dacewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bari mu kalli manufofin da gwamnatin Donald Trump ta aiwatar a yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin misali. A bayyane ne ta ba da kwarin gwiwa ga Isra’ila kan batun Palasdinu da Isra’ila, lamarin da ya ba da damar sake barkewar rikici a tsakanin bangarorin 2. Dawo da ofishin jakadancin Amurka da ke Isra’ila daga Tel Aviv zuwa Kudus, amincewa da mayar da Kudus a matsayin hedkwatar Isra’ila, gabatar da sabon shirin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, inda ta nuna goyon baya ga Isra’ila, amincewa da halatattun matsugunan Yahudawa, da dakatar da ba da taimakon kudi ga ofishin MDD mai kula da ba da agaji ga ‘yan gudun hijira a yankin gabas ta tsakiya, dukkan wadannan matakan da Amurka ta dauka sun sha saba sharudda, abin da ke kara ta'azzara yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

A daidai wannan lokaci, shawarwari guda 4 da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2017 dangane da daidaita batun Palasdinu, suna da ma’ana mai muhimmanci. Saboda haka a yayin muhawarar da aka yi a ranar 16 ga wata, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tsagaita bude wuta, abu ne da tilas ake bukata cikin gaggawa. Sa’an nan akwai matukar bukatar ba da agajin jin kai. Kamata ya yi kasashen duniya su ba da nasu goyon baya. Shirin kafa kasashe guda 2, ita ce hanya daya tilo da za a bi. Har ila yau, kasar Sin ta sake nanata gayyatar masu kishin zaman lafiya daga Palasdinu da Isra’ila da su zo kasar Sin don yin tattaunawa, kasar Sin tana maraba da Palasdinu da Isra’ila da su yi tattaunawa fuska da fuska a kasar Sin.

Kowa ya ga sahihanci da kokarin da kasar Sin take yi wajen sassauta rikicin da ke faruwa a Palasdinu da Isra’ila, lamarin da ya nuna yadda kasar Sin ta cika alkawainta na kokarin shimfida zaman lafiya a duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan