Hare-haren sojojin Isra'ila kan sassan soja na kungiyar Hamas
2021-05-11 19:45:07 CRI
A daren jiya, rundunar sojojin Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa, sojojin ta sun kai hare-hare kan sassan soja da dama na kungiyar Hamas da ke zirin Gaza. A cewar jami’an lafiya na Palasdinu, hare-haren sun halaka Palasdinawa 20, ciki har da yara 9.(Lubabatu)