logo

HAUSA

Kasar Sin ta nemi al'ummomin kasa da kasa su ingiza tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu

2020-09-30 10:03:22 cri

Mataimakin zaunannen jakadan kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya nemi kasashen duniya su ingiza tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

A jawabinsa yayin babban taron MDD a makon da ya gabata, shugaban Falasdinu, Mahmud Abbas, ya yi kira ga Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres, ya hada hannu da kasashe mambobin kwamitin sulhu da bangarorin nan 4 masu shiga tsakani kan batun gabas ta tsakiya, wajen shirya babban taron kasa da kasa a farkon badi, domin tattauna sahihiyar hanyar samar da zaman lafiya.

Geng Shuang, ya ce Sin ta yi ammana cewa, wannan kira ya nuna kyakkyawan kudurin Falasdinu na shiga tattaunawar sulhu da inganta zaman lafiya. Ya ce ya kamata dukkan bangarori su ba batun muhimmanci, sannan su duba yuwuwar samar da kyakkyawan yanayi warware batun Falasdinu a siyasance.

Jakadan ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa musamman kasashen dake da tasiri kan Falasdinu da Isra'ila, su samar da matsaya mai ma'ana bisa adalci, da za ta inganta tattaunawar sulhu da ma batun wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Shugaban na Falasdinu ya kuma bayyana cewa, kasarsa na shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki, inda zai kunshi dukkan jam'iyyun siyasar kasar, lamarin da jakada Geng Shuang ya ce Sin na maraba da shi, kuma tana sa ran ganin an samu nasarar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu da sauran harkokin siyasa. (Fa'iza Mustapha)