logo

HAUSA

Sudan ta sanar da fara kulla yarjejeniyar cinikayya da Isra'ila a hukumance

2020-10-26 10:31:33 cri

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan, ta sanar da kulla yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar da Isra'ila, wadda za ta fara da hadin gwiwa a fannin aikin gona.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce Sudan da Isra'ila, sun yanke shawarar kawo karshen tsamin dangantaka a tsakaninsu, inda suka dawo da dangantaka ta hanyar farawa da yarjeniyoyin cinikayya da tattalin arziki, wadanda suka mayar da hankali kan aikin gona, domin amfanawa al'ummomin kasashen biyu.

Ma'aikatar ta kara da sanar da cewa, za a gudanar da taro tsakanin wakilan kasashen biyu cikin makonni masu zuwa.

Ta ce manufar taron ita ce, cimma yarjejeniyar hadin gwiwa a fannonin da suka shafi aikin gona da cinikayya da tattalin arziki da sufurin jiragen sama da harkokin shige da fice da sauran wasu fannoni, da nufin cimma muradun al'ummomin kasashen biyu.

Har ila yau, sanarwar ta ce Amurka da Isra'ila, sun bayyana niyyarsu ta taimakawa Sudan wajen inganta wadatar abinci a kasar da lalubo damammakin tattalin arziki da take da su da yakar da ta'addanci da kaifin kishin addini. (Fa'iza Mustapha)