logo

HAUSA

Isra'ila da Sudan sun amince da dawo da huldar diflomasiyya a tsakaninsu

2020-10-24 16:02:57 cri

Isra'ila da Sudan, sun amince su dawo da dangantaka a tsakaninsu, yayin da shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da majalisar wakilan kasar ta cire Sudan daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ta'addanci.

Wata sanarwar hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila da Sudan suka fitar, ta ce shugabannin sun amince da sabunta dangantaka tsakanin Sudan da Isra'ila da nufin kawo karshen zaman doya da manja dake tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta ce shugabannin sun kuma amince da fara huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, inda za su fara mayar da hankali ga fannin aikin gona.

Ta kara da cewa, wannan mataki zai inganta tsaro a yankin tare da bude sabbin kofofin damarmaki ga al'ummun Sudan da Isra'ila da Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afrika.

Yayin tattaunawar da aka yi ta wayar tarho tsakanin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da takwaransa na Sudan, Abdalla Hamdok da Shugaban Amurka Donald Trump, shugaba Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ta zaman lafiya, yana mai cewa karin kasashen Larabawa za su bi sahu. (Fa'iza Mustapha)