logo

HAUSA

Ghana ta zama kasar farko da ta karbi riga-kafin COVAX

2021-02-25 10:19:53 CRI

A jiya Laraba gwamnatin kasar Ghana ta karbi riga-kafin annobar COVID-19 kimanin 600,000 na kamfanin AstraZeneca wanda cibiyar hada magunguna ta Serum ta kasar India ta samar, inda ta zama kasar farko da ta karbi riga-kafin cutar COVID-19 karkashin shirin COVAX na raba daidai na alluran riga-kafin ga kasashe masu karamin karfi a duniya.

A wata sanarwar hadin gwiwa ta asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF da hukumar lafiya ta duniya WHO, an bayyana cewa, sun yi matukar farin ciki kasancewar Ghana ta zamto kasa ta farko da ta karbi riga-kafin cutar COVID-19 karkashin shirin COVAX. A matsayinsu na tawagar MDD dake aiki a Ghana, UNICEF da WHO, sun jaddada aniyarsu na taimakawa shirin samar da riga-kafi da kuma dakile bazuwar annobar, ta hanyar hadin gwiwa ta kut-da-kut da dukkan bangarori.

Ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya ce gwamnati za ta gudanar da riga-kafin cutar COVID-19 ne rukuni-rukuni a tsakanin jama’ar kasar tun daga mako mai zuwa, inda ya bukaci al’ummar kasar da su sa himma wajen karbar riga-kafin da zarar an fara.(Ahmad)

Ahmad