logo

HAUSA

An rantsar da Akufo Addo a karo na biyu a matsayin shugaban kasar Ghana

2021-01-08 10:23:04 CRI

An rantsar da shugaban kasar Ghana Nana Dankwa Akufo Addo a jiya Talata, domin fara aiki a wa’adin mulki na biyu.

Babban alkalin kasar Kwasi Anin Yeboh ne ya rantsar da shi a gaban wasu shugabannin kasashe 12 dake ziyara a kasar da kuma wasu manyan baki daga ciki da wajen kasar.

Da yake jawabi, Shugaba Akufo Addo, ya ce sake zabarsa da aka yi alama ce dake nuna cewa al’ummar kasar sun aminta da shi, da yabawa da nasarorin da aka samu a wa’adin mulkinsa na farko da kuma sauran ayyukan da za a yi cikin shekaru 4 masu zuwa.

Ya jaddada bukatar dora kasar kan tafarkin ci gaba da kwanciyar hankali biyo bayan tasirin annobar COVID-19, yana mai tabbatarwa al’ummarsa cewa, zai yi iya kokarinsa domin cimma wannan buri.

Shugaban ya kara da cewa, za a cimma tsarin demokradiyyar da kasar ta yammacin Afrika ke kokarin ginawa ne idan aka samu ci gaba, kana aka samu zaman lafiya a tsakanin mutane da kuma duniya. (Fa’iza Mustapha)