logo

HAUSA

Biden ya ba da umurnin kai hari ta sama kan dakarun Sham dake samun goyon baya daga Iran

2021-02-26 10:24:36 CRI

Kafar yada labarai ta AP, ta ba da labari jiya cewa, shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya ba da umurnin kai hari ta sama kan rundunar sojojin sa kai dake kasar Sham, wadda ke samun goyon bayan kasar Iran.

Hukumar tsaron kasar Amurka ta ba da labari a wannan rana cewa, sojinta sun kai hari kan na’urori da dama, na rundunar dakarun sa kai wadda ke gabashin kasar Sham.

A wani bangare kuma, rundunar sojojin gwamnatin Sham, ta shaidawa manema labarai na CMG cewa, a daren wannan rana, an kai hari ta sama sau da dama, a gabashin kasar dake dab da kasar Iran.  (Amina Xu)