logo

HAUSA

Ba Wanda Zai Hana Tasowar Kasar Sin, Balle Joseph Biden

2021-03-26 15:11:59 CRI

Ba Wanda Zai Hana Tasowar Kasar Sin, Balle Joseph Biden_fororder_7672141312443041549

Shaharraren masanin tattalin arziki na Amurka, Richard Wolf, ya shedawa manema labarai na gidan telibiji na Russia Today cewa, Sin tana kokarin tasowa, inda ta kusan zarce Amurka a cikin shekaru 30 da suka gabata, yana mai cewa kamata ya yi Amurka ta san wannan ci gaba, amma gwamnatinta tana son hana bunkasuwar kasar Sin. Matakin da ba zai samu nasara ba ko kadan, ya ce Donald Trump ya gaza yin haka, balle ma gwamnatin Biden.

Yayin da ya yi tsokaci kan huldar kasashen biyu a fannin ciniki da tattalin arziki, Wolf ya nuna cewa, a cikin shekarun baya-bayan nan, bangarorin biyu sun ci gajiyar nagartacciyar huldar a wannan fannin, amma tun lokacin da Donald Trump ya hau kujerar shugaban kasar, sai gwamnatinsa ta dauki matakan da ba su dace ba kan kasar Sin.

A cewarsa, bai san dalilin da ya sa gwamnatin Trump da ta Biden suka yi watsi da dangantaka mai amfanawa juna, suka zabi hanyar yin fito-na fito da kasar Sin ba. A ganinsa, wadannan matakai tamkar fusata ne ko damuwa da tasowar kasar Sin, ganin cewa har ta kusan zarce Amurka. (Amina Xu)