logo

HAUSA

Biden zai janye jikin sojojin Amurka daga Afghanistan nan da 11 ga watan Satumba

2021-04-14 10:17:17 CRI

Biden zai janye jikin sojojin Amurka daga Afghanistan nan da 11 ga watan Satumba_fororder_210414-sojojin Amurka

Rahotanni daga Amurka na cewa, shugaban kasar Joe Biden, zai samar da janye sojojin kasar dake kasar Afghanistan nan da ranar 11 ga watan Satumban wannan shekara.

Jaridar Washington Post ta ba da rahoton cewa, a yau ne ake sa ran shugaba Biden zai sanar da wannan shawara, matakin da zai kara kasancewar sojojin na Amurka a Afghanistan fiye da ranar 1 ga watan Mayu da aka cimma yarjejenitar tsakanin tsohuwar gwamnatin Amurka da kungiyar Taliban dake Afghanistan.

Ranar 11 ga watan na Satumba dake tafe, ta yi dai-dai ta cika shekaru 20 da hare-haren ta’addancin nan da ya jefa kasar ta Amurka cikin yaki a Afghanistan, yaki mafi tsawo a tarihin kasar Amurka.

Biden ya bayyana a watan da ya gabata cewa, abu ne mai wahala Amurka ta cika wa’adin ranar 1 ga watan Mayu na janye sojojinta daga Afghanistan, “saboda dalilai na dabarun aikin soja”.

Ma’aikatan tsaron Amurka ta Pentagon, ta bayyana cewa, akwai zaratan sojojin Amurka 2,500 a kasar Afghanistan, amma a baya-bayan nan kafofin watsa labaran kasar, sun bayyana cewa, wannan adadi bai hada da karin sojojin musamman na Amurka 1,000 dake kasar ta Afghanistan ba. (Ibrahim)