logo

HAUSA

Sin ta shawarci Japan da ta janye kudurin ta na zubar da dagwalon nukiliya cikin teku ta kuma nemi afuwa

2021-04-28 21:14:28 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya yi kira ga gwamnatin kasar Japan, da ta janye kudurin ta na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar tashar Fukushima cikin teku, ta kuma nemi afuwar ayyana wannan mataki da ta yi.

Zhao ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, lokacin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da wani sakon tiwita da ya wallafa a shafin sa a ranar Litinin.

Sakon na tiwita dai na kunshe ne da zanen wani tsohon sanannen zanen kasar Japan mai lakabin "Babbar igiyar ruwa ta Kanagawa", ya kuma nuna yadda ake juye ruwan sinadarin nukiliya cikin teku.

To sai dai kuma a jiya Talatar, Japan ta nuna adawar ta da wannan sako na tiwita, tana kira da a janye shi. Bayan hakan ne kuma Zhao ya kare sakon na sa, yana mai cewa, ya makala wannan sako ne a jikin shafin sa. Ya ce ita ma Japan ta aikata munanan abubuwa. Abun tambaya kuma shi ne, shin ba wanda ke da damar cewa wani abu game da hakan ke nan?  (Saminu)

Saminu