logo

HAUSA

Sin ta yi watsi da zarge zargen Japan

2021-04-27 20:31:25 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa ta gabatar da korafi ta hanyoyin diflomasiyya ga kasar Japan, bisa wasu bayanai da Japan din ta wallafa cikin wani kundin musamman da ta fitar a Talatar nan, mai kunshe da yayata zargin da wasu sassa ke yiwa kasar Sin na kasancewa barazana gare su.

Wang Wenbin, wanda ya yi wannan tsokaci a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce kundin na kunshe da karairayi masu bata sunan kasar Sin, da kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar.

To sai dai kuma kundin ya ce alakar Japan da kasar Sin tana da matukar muhimmanci, kalaman da Wang Wenbin ya ce bai dace an fade su da fatar baki ba kaiwa, maimakon hakan, kamata ya yi bangaren Japan ya aiwatar da su a zahiri.

Jami’in ya kara da cewa, a yanzu haka dangantakar Sin da Japan na fuskantar babban kalubale, kuma Sin na kira ga gwamnatin Japan da ta gyara kurakuran ta, ta karkata akalar ta zuwa gina kyakkyawar dangantaka da Sin, ta hanyar aiwatar da matakai na zahiri. (Saminu)

Saminu