logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin: Ya kamata Japan ta yi taka tsan-tsan yayin da take kula da batun gurbataccen ruwa na tashar nukiliya ta Fukushima

2021-04-22 10:19:18 CRI

Ministan harkokin wajen kasar Sin: Ya kamata Japan ta yi taka tsan-tsan yayin da take kula da batun gurbataccen ruwa na tashar nukiliya ta Fukushima_fororder_0422-bell-1

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta da takwaransa na kasar Jamus Heiko Maas ta kafar bidiyo, inda jami’an biyu sun tattauna batun zubar da gurbataccen ruwan tashar nukiliya ta Fukushima da ta lalace, da gwamnatin kasar Japan ke neman gudanarwa.

Yayin zantawar ta su a jiya Laraba, Mista Wang ya ce, gwamnatin kasar Japan ba ta gwada sauran matakai marasa hadari ba, kana ba ta bayyana dukkan bayanai a fili ba. Maimakon haka tana shirin zubar da gurbataccen ruwa mai kunshe da gubar nukiliya cikin teku, ba tare da tattaunawa da kasashe makwabta, da gamayyar kasa da kasa ba.

Hakan, a cewar Wang, zai haifar da illa ga jama’ar kasashe makwabtan kasar Japan, da barazana ga muhallin halittu, da tsaron lafiyar jama’ar kasashe daban daban.

Wang ya kara da cewa, ya kamata kasar Japan ta yi kokarin mayar da martani ga damuwar da jama’ar kasashe daban daban suka nuna, da dora cikakken muhimmanci kan moriyar bai daya ta kasashen duniya, da sauke nauyin dake bisa wuyanta. Sa’an nan ta yi taka tsan-tsan yayin da take kula da batun, musamman ma bukatar da ake yi mata na yin cikakkiyar tattaunawa tare da bangarori masu ruwa da tsaki, da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. (Bello Wang)

Bello