logo

HAUSA

Dole Ne Japan Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Domin Moriyar Bil Adama Baki Daya

2021-04-21 11:21:17 CRI

Dole Ne Japan Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Domin Moriyar Bil Adama Baki Daya_fororder_japan

Kwanan baya, wasu Japanawa sun yi shelar cewa, ma’aunin da kasashen Sin da Koriya ta Kudu suke bi ta fannin daidaita gurbataccen ruwa daga tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya bai kai na kasar Japan ba. Dalilin da ya sa Japan ta yi haka shi ne domin yunkurin rufe gaskiya, wato gurbataccen ruwa daga tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta Fukushima ya sha bamban da ruwan da ake fitarwa daga tasoshin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya. Japan ta boye illolin gurbataccen ruwan daga tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta Fukushima, a yunkurin halatta kudurinta na zuba irin wannan gurbataccen ruwa cikin teku.

Masana kimiyya daga kasa da kasa sun ba da misalan abubuwa masu ban tausayi da za su wakana a nan gaba a tekun, idan Japan ta zuba gurbataccen ruwan. Hakika dai, akwai sauran hanyoyi masu dacewa da Japan za ta bi wajen daidaita gurbataccen ruwan, amma tana son yin tsimin kudi, a maimakon wanzar da tsaron lafiya a duniya. Za ta kawo wa lafiyar dukkan bil Adam barazana a maimakon sauke nauyinta yadda ya kamata. Ta tsai da kudurinta ne ba tare da tunani ba.

Kada gwamnatin Japan ta sake yin abubuwa na rashin tunani! Ya zuwa yanzu wasu Japanawa ba su nemi gafara daga kasashe masu makwabtaka da ita bisa abubuwan da Japan ta aikata a yakin duniya na 2 ba. Yanzu kuma muddin Japan ta zuba gurbataccen ruwan cikin teku, to, illolin da zai yi sun fi illolin da wani yaki zai yi muni. Ya zama tilas Japan ta sake yin tunani kan kudurinta, ta kuma gyara kuskure, ta soke kudurinta, ta kuma sauke nauyinta domin makomar ‘yan Adam da zuriyoyi. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan