logo

HAUSA

Sin: Ya kamata Japan ta saurari adawar da kasashen duniuya suka nuna ta gyara mummunan shawarar da ta yanke na zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliyarta a cikin teku

2021-04-20 20:24:02 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya karyata ikirarin da kasar Japan ta yi cewa, wai mizanin yadda ake tace gurbataccen ruwa a tashohin makamashin nukiliya a kasashen Sin da Koriya ta kudu, ba su kai na wadanda ke kasarta ba.

Wang wanda ya bayyana haka yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Talatar nan, ya kuma jaddada cewa, bangaren Japan ya fitar da sanarwar da abin da ya shafa ne, a matsayin wani salo na sauya ra’ayi da janye hankalin duniya. Abin da ya dace Japan ta yi a halin yanzu, ba wai ta rudar da jama’a da sunan batu na kimiyya ba, kamata ya yi ta kawar da duk wani shakku da duniya ke nunawa kan wannan mummunan mataki nata, da ma yadda duniya ke adawa da akidarta ta kimiyya, ta kuma hanzarta sauke nauyi na kasa da kasa dake bisa wuyanta, ta gyara kuskuren shawarar da ta yanke na zubar da dagwalon ruwan tashar nukiliyar Fukushima da ta gamu da hadari a cikin teku, da samun tabbacin kasashe makwabatanta da kungiyoyin kasa da kasa.