logo

HAUSA

Anya Japan ta damu da korafin al’ummarta da na sauran jama’ar da shirinta zai yi tasiri a kansu?

2021-04-20 19:07:04 cri

Anya Japan ta damu da korafin al’ummarta da na sauran jama’ar da shirinta zai yi tasiri a kansu?_fororder_微信图片_20210420190634

Kwararru daga bangarori daban daban na majalisar Dinkin Duniya da suka hada da na bangarorin  kula da sinadarai masu guba da kare hakkin dan adam, da na da kula da abinci da kuma na kare hakkin bil Adam da kare muhalli, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana matukar damuwa dangane da yawan gurbataccen ruwan da ya kai ton miliyan 1 da zai iya haifar da gagarumin barazana ko hadari ga rayukan jama’a, wanda kasar Japan ta tsaya kai da fata sai ta zuba cikin teku, duk adawar da aka bayyana.

A baya-bayan nan ne, gwamnatin kasar Japan ta sanar da yanke shawarar zubar da ruwan dagwalon cibiyar makamashinta ta Fukushima mai cike da sinadarai masu guba cikin teku Fasifik, duk kuwa da adawar da aka nuna daga ciki da wajen kasar. Japan dai ta tara ruwa mai tururin guba mai yawan gaske, tun bayan hadarin tashar nukiliyar da ta faru a shekarar 2011, sakamakon girgizar kasa da igiyar ruwa ta tsunami.

A yayin da ake kiraye-kirayen kare muhalli, kuma kasa da kasa suka dukufa wajen ganin sun tunkari matsalolin muhalli da na yanayi da ake fuskanta a wannan zamani, kasar Japan ta bullo da wannan shiri, wanda ko alama babu cewa, ta yi la’akari da mummunan tasirin da matakin nata zai haifar.

Tekun Fasifik na iyaka da kasashe sama da 40 kana yana dauke da tsibirai mafi yawa na duniya. Yanzu haka, tarin bolar dake cikin tekun kadai ya isa tayar da hankali bare kuma an kara da tarin sinadarai masu guba da za su iya halaka halittu da albarkatun cikin ruwan tare da illa ga jama’a. Abun mamaki shi ne, matakin na Japan, na fsukantar adawa daga cikin kasar, musamman daga kungiyar masu kamun kifi, amma kuma sai ta yi biris da muradunsu, inda ta mayar da hankali kadai kan shawarar da ta yanke. To wani irin alfanu kasa za ta samu idan ta gaza mayar da hankali kan bukatun al’ummarta ko kuma ita da kanta ta tsohe musu hanyar samun kudin shiga da kuma abinci? Ina kuma ga sauran al’ummomin dake kewaye da tekun?

A wannan lokaci, kasashe sun dukufa, suna kokarin kyautata muhalli, inda kasa kamar Sin ke ingantawa da ba da gwarin gwiwa tare da daukan tsauraran matakan farfado da muhalli da tsaftace koguna domin moriyar al’umma. Aikin tsaftacewa da farfado da kogin Yangtze kadai, ya isa misali na irin wannan yunkuri. To amma a wannan gabar ne kuma wata kasa ta bullo da wata bahaguwar dabara ta mayar da hannun agogo baya.

Shi ya sa a matsayinta na babbar kasa kuma makwabciya ga Japan, kasar Sin, tare da Kasar Koriya ta kudu da kasar Koriya ta arewa, suka bayyana takaicinsu dangane da matakin na Japan, inda suka yi kira gare ta, ta daidaita batun ta hanyar hawa teburin tattaunawa da kasashe masu ruwa da tsaki domin daukar matakan da suka dace. Haka kuma sun lashi takobin mayar da martani kan wannan kalubale.

Yunkurin na Japan tamkar takalar fada ne da haifar da zaman dardar a yankin. Bai kamata Japan ta ce za ta dauki amincewar Amurka kan wannan batu a matsayin wani dalili, na samun nutsuwa game da matakin da take shirin aiwatarwa ba. Matsalar da matakin zai haifar, ita zai shafa da al’ummarta da sauran kasashen yankin da al’ummarsu amma ba Amurka ba. Ya kamata ta fahimci cewa, ko kadan Amurka dake ingiza ta, ba ta da asara. Adawar kadai da al’ummar kasar suka nuna, ya isa ya sanya Japan din sake shawara tare da lalubo mafita mafi dacewa da za ta karbu ga kowa dangane da shirin nata. (Faeza Mustapha)