logo

HAUSA

Yakin Afghanistan, Dandali Ne Na Nuna Mummunan Sakamako Na Kutsa Kai Da Amurka Ta Yi

2021-04-27 20:55:55 CRI

Yakin Afghanistan, Dandali Ne Na Nuna Mummunan Sakamako Na Kutsa Kai Da Amurka Ta Yi_fororder_amurka

Kwanan baya, kwamandan rundunar sojan Amurka da ke Afghanistan ya fayyace cewa, Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, sun fara janye sojoji daga wasu sansanoninsu dake Afghanistan.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, za su kammala aikin janyewar ne kafin ranar 11 ga watan Satumban bana. Lamarin ya nuna cewa, wannan yaki da Amurka ta tayar da shi bisa sunan yaki da ‘yan ta’adda, aka kuma dauki shekaru 20 ana yinsa zai kawo karshe. Abin da ya rage shi ne Afghanistan, wadda ke cikin mawuyancin hali.

Alkaluman bankin raya Asiya sun nuna cewa, mutanen Afghanistan da yawansu ya kai kaso 54.5% suna fama da kangin talauci. Mutanen da suka cancanci yin aiki wadanda yawansu ya kai 40.1%, yawan kudin shigarsu a ko wace rana bai kai dalar Amurka 2 ba a Afghanistan.

A cikin shekaru 20 da suka wuce, Amurka ta zuba dalar Amurka triliyan 2 kan yakin Afghanistan baki daya, yayin da sojojinta fiye da 2400 suka rasa rayukansu.

Yadda Amurka za ta sa aya ga yakin Afghanistan ya alamta cewa, yunkurinta ya ci tura baki daya a yakin Afghanistan. Salon dimokuradiyya irin na Amurka bai cancanci Afghanistan ba. Haka kuma Amurka ta samu mummunan sakamako daga ta da kura, da kutsa kai cikin wata kasa ta daban.

Ga yadda duniyarmu take kasancewa yanzu, dukkan kasashen da Amurka ta kutsa kai bisa karfin soja, suna fama da rashin kwanciyar hankali da ci gaba, inda kuma al’umma suke cikin mawuyancin hali.

Kasashen duniya suna fahimtar cewa, Amurka ta zama wadda ta fi gurgunta yanayin kwanciyar hankali a duniya, inda ta tsoma baki cikin wata kasa ta daban da sunan “shimfida dimokuradiyya”, ta kuma haddasa bala’un kare hakkin dan Adam da sunan “kiyaye hakkin dan Adam”.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan