logo

HAUSA

Wang Yi: Amurka ta kasa warware bambance dake tsakaninta da Sin

2021-04-27 15:27:59 CRI

Wang Yi: Amurka ta kasa warware bambance dake tsakaninta da Sin_fororder_王毅

Jaridar the Economic Times ta kasar Indiya ta ruwaito cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, har yanzu Amurka ta gaza samo hanyar da ta dace ta warware bambance-bambance dake tsakanin kasashen biyu. Kalaman ministan na zuwa ne, yayin da Amurka ke tsoma baki a harkokin yankin Taiwan na kasar Sin, wanda har Sin din da gargade ta cewa, “wasa da batun Taiwan, tamkar wasa da wuta ne”.

Wang Yi, wanda har ila mamba ne a majalisar gudanarwar kasar, ya bayyana haka ne ranar Jumm’ar da ta gabata, yayin taron masu ruwa da tsaki na Amurka a fannin huldar kasashen waje, wanda ya gudana ta kafar bidiyo.

Kasar Sin na fatan gwamnatin Biden za ta kalli wannan batu da idon basira, ta kuma fahimci hanyar bunkasuwar kasar Sin ta sabuwar hanyar zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna.(Ibrahim)