logo

HAUSA

Ana bacin rai game da yadda Amurka ke mallake rigakafin fiye da kima yayin da annoba ke kara kamari a duniya

2021-04-27 14:25:16 CRI

Ana bacin rai game da yadda Amurka ke mallake rigakafin fiye da kima yayin da annoba ke kara kamari a duniya_fororder_疫苗-5

Jaridar The Washington Post ta kasar Amurka ta ce, yayin da kasar Indiya ta samu adadi mafi yawa na mutanen dake kamuwa da annobar COVID-19 a rana guda, ita kuwa kasar Amurka na kara mallake alluran rigakafin cutar.

A kasar ta Indiya, kashi 1.4 bisa 100 na yawan al’ummar kasar ne kadai suka samu cikakkun rigakafin, yayin da asibitocin kasar ke fama da karancin iskar oxygen. A kasar ta Amurka mutum guda cikin Amurkawa 4 ya riga ya samu cikakkun rigakafin, sannan sama da kashi 40 bisa 100 na mutanen kasar sun karbi zagayen farko na rigakafin, asibitin Jackson Memorial dake Miami, ya bayyana cewa, zai fara dakatar da aikin rigakafin saboda alluran da ake samarwa na kara yin yawa, kana masu bukatar rigakafin na ci gaba da raguwa.(Ahmad)