logo

HAUSA

Kila ne shugabannin Rasha da Amurka za su gana a watan Yuni

2021-04-26 11:40:24 CRI

Kila ne shugabannin Rasha da Amurka za su gana a watan Yuni_fororder_hoto

Mai taimakawa shugaban kasar Rasha Yury Ushakov ya bayyana a jiya Lahadi cewa, mai iyuwa, shugaban kasarsa Vladimir Putin zai gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, a watan Yuni mai zuwa.

Ya ce, kasar Amurka ta nuna fatan ganawar shugabannin biyu, amma, ba a tsai da kuduri na karshe kan ko za a yi wannan ganawa ko a’a ba, domin ba a fara aiwatar da ayyukan da suka shafi batun ba. Ya ce, mai iyuwa, shugabannin biyu za su gana a watan Yuni, ko wata rana ta musamman, amma, bai yi karin bayani kan ranar ba.

Ban da haka kuma, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana a jiya Lahadi cewa, yanzu, kasar Rasha tana tsara wani jerin kasashen da ba su sonta, kuma, tabbas Amurka tana cikin wannan jeri, domin Rashar ta tsai da kudurin tsara jerin ne bisa matakai marasa kyau da dama da Amurka ta dauka kanta. (Maryam)