logo

HAUSA

Jaridar Hong Kong: Yakin da Sin ke yi da ta’addanci, abin da kasashen yamma ba su fada muku game da hakikanin halin da ake ciki a Xinjiang

2021-04-25 16:25:12 CRI

Jaridar Hong Kong: Yakin da Sin ke yi da ta’addanci, abin da kasashen yamma ba su fada muku game da hakikanin halin da ake ciki a Xinjiang_fororder_新疆02

Jaridar South China Morning Post, dake da babban ofishinta a yankin Hong Kong na kasar Sin, ta wallafa wani sharhi a ranar 14 ga watan Afrilu mai taken, “yakin da kasar Sin ke yi da ta’addanci, abin da kasashen yammacin duniya ba su fada muku game da yankin Xinjiang. Sharhin na cewa, ba kamar yakin da kasar Amurka ke yi da ta’addanci ba, yaki da ta’addancin da kasar Sin ke yi yana da amfani. Ba a samu rahoto game da hare haren ta’addanci ba tun daga shekarar 2017. Gaskiyar batun shi ne, kasar Sin ta samu nasarar dakile wannan babbar matsala wacce ke addabar duniya ta ayyukan ta’addanci ba tare da haifar da mummunar barna ba, wannan hakika babban abin yabawa ne. Wannan ba a taba jin kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya suna bayyanawa ba.

A halin yanzu Amurka tana zargin kasar Sin da aikata kisan kiyashi ba tare da wata hujja ba. Shin laifi ne idan kasar Sin ta zargi Amurka da yin fuska biyu?

Manufofin kasar Sin game da yankin Xinjiang ba wai ana aiwatar da shi kan wani addini ko wata kabila ba ne, sai dai kan masu tsattsauran ra’ayi kawai. Manyan kasashen musulmai sun fahimci hakan kuma suna goyon bayan kasar Sin kan hakan.(Ahmad)

Ahmad Fagam