Manoman Xinjiang sun samu karin kudin shiga daga noman Almonds
2021-04-17 16:12:12 CRI
Gundumar Shache, ta jihar Xinjiang ta kasar Sin, sansani ne na noman Almonds mafi girma a kasar Sin, wadda akewa lakabi da “garin Almonds”, inda ake noman Almonds din a gonaki masu fadin hekta sama da dubu 66. A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, manoman gundumar sun samu karin kudin shiga daga noman Almonds.
Misali, manomi Tohti Turdi ya je kamfanin Ameti da aka kafa a gundumar, dauke da gyadar Almonds da ya ajiye a cikin jakuna da dama domin sayar da su, inda manajan kamfanin, Muhtarjan Mulaniyaz ya saye duka.
Yanzu kamfanin Ameti yana sayar da Almonds zuwa ga birnin Tianjin da lardin Henan da lardin Anhui da sauran lardunan kasar. A ko wace shekara, adadin kudin da kamfanin yake samu daga sayar da Almonds ya kai kudin Sin yuan biliyan daya, a sa’i daya kuma, kamfanin yana samar da guraben aikin yi ga matasan iyalan dake fama da talauci, har ya kai su ga fita daga kangin talauci.(Jamila)