logo

HAUSA

Mutane da dama za su fadi gaskiya game da Xinjiang

2021-04-23 21:33:20 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Jumma’a cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, mutane da dama da ke nuna adalci da gaskiya daga cikin kasashen duniya, za su fito su fadi gaskiya su kuma yi magana ba tare da nuna son kai ba game da Xinjiang.

Rahotanni na cewa, tashar yanar gizo ta wani sanannen wurin musamman da aka kebe a shafin "Project Syndicate" kwanan nan ya wallafa labari mai taken "Zargin kisan kare dangi a Xinjiang ba shi da tushe", inda ya bayyana cewa, Amurka ta zargi kasar Sin da aikata "kisan gillar" a Xinjiang ba tare da wata hujja ba, ya kuma yi kira ga gwamnatin Amurka da ta canza halayyarta, ta yi watsi da zargin karya da ta ke yi. (Bilkisu)