logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da kudurin da majalisar wakilan Birtaniya ta zartas kan yankin Xinjiang na kasar Sin

2021-04-23 14:34:41 CRI

 

Kakakin ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya ya shedawa manema labarai a jiya Alhamis cewa, kudurin da wasu wakilan majalisar wakilan kasar suka zartas da shi dangane da yankin Xinjiang na kasar Sin a wannan rana, ta keta dokar kasa da kasa da ka’idar huldar duniya, kuma shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, don haka Sin ta yi Allah wadai da hakan da kakkausar murya.

Kakakin ya ce, karyar da aka yi wai an yiwa ‘yan kabilar Uygur kisan kare dangi, ta saba da hakikanin halin da ake ciki a yankin Xinjiang, kuma ta shafawa kasar Sin bakin fenti kan ci gaban da take samu wajen daidaita harkokin yankin. Ya ce ainihin abun da ya kamata a warware a yankin shi ne, yaki da ta’addanci da kawar da tsattsauran ra’ayi da adawa da kawo baraka, abin dake da alaka matuka da ikon mulki da cikakken ‘yancin kasar Sin. Bayan namijin kokarin da al’umomin Sin suka yi, yankin bai fuskanci ayyukan ta’addanci ba a cikin fiye da shekaru 4 da suka gabata, ban da wannan kuma ana samun kwanciyar hankali da ci gaba mai wadata, abin da ya kyautata zaman rayuwar jama’a. A shekarun baya-baya nan, yawan al’ummar Uygur ya rika karuwa, jama’a suna gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, kuma an kiyaye harsuan da al’adun gargajiya da ma kabilun yankin da sauransu.

Ya kara da cewa, duk abubuwa sun shaida cewa, babu kisan kare-dangi, kuma Sin ba ta taba aikata laifin cin zarafin dan Adam ba. Ya ce ikirarin da ake yi wai akwai matsalar kisan kare-dangi a yankin, mataki ne da aka dauka na fakewa da batun hakkin Bil Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. (Amina Xu)