logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da Japan su daina shisshigi a harkokin cikin gidanta

2021-04-18 17:14:50 CRI

A jiya Asabar, kasar Sin ta bukaci kasashen Amurka da Japan da su daina yin katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana su kaucewa lahanta moriyar kasar ta Sin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya kamata Amurka da Japan su dauki batun dake shafar kasar Sin da muhimmanci, su kiyaye manufar kasar Sin daya tak a duniya, kana su gaggauta kaucewa yin shisshigi a harkokin cikin gidan Sin da gujewa lahanta moriyar kasar Sin. Kasar Sin zata dauki dukkan matakan da suka dace domin kare ikon kasarta, da tsaronta, da kuma moriyarta.

Kakakin ya bayyana hakan ne a lokacin da aka nemi ya yi tsokaci game da sanarwar hadin gwiwar da shugabannin Amurka da Japan suka fidda, wacce aka fitar bayan kammala wani taron da suka gudanar, inda suka bayyana damuwa dangane da batutuwan dake shafar yankin Taiwan, da tsibirin Diaoyu, da Hong Kong, da Xinjiang da kuma batun tekun kudancin kasar Sin.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Sin, yankin Taiwan da tsibirin Diaoyu dukkansu yankunan kasar Sin ne, ya kara da cewa, batutuwan dake shafar Hong Kong da Xinjiang al’amurra ne na cikin gidan kasar Sin, kuma babu shakka game da batun ikon da kasar Sin take da shi a tsibirranta da ke tekun kudancin kasar, gami da haddin ruwan dake kewaye dasu.

Kakakin ya jaddada cewa, sanarwar hadin gwiwar shugabannin Amurkar da Japan ta yi shisshigi matuka game da harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ta sabawa dokokin da ke shafar huldar kasa da kasa.(Ahmad)