logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Amurka da Japan ba za su iya wakiltar kasashen duniya ba

2021-04-19 21:28:56 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Amurka da Japan ba za su iya wakiltar kasashen duniya ba_fororder_1

Game da ra’ayoyin da shugabannin kasashen Amurka da Japan suka nuna a yayin ganawa da suka yi kwanan nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya sake jaddada matsayin kasarsa a yau Litinin, inda ya nanata cewa, Amurka da Japan ba za su wakilci sauran kasashe ba, kana, ba su cancanci su tsara ka’idojin kasa da kasa ba, kana ba su cancanci tilastawa sauran kasashe su amince da nasu matsayi ba.

Wang Wenbin ya kara da cewa, akwai tsari daya kacal a duniya, wato tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Akwai kuma ka’ida daya a duniya, wato babbar ka’idar da ta shafi huldodin kasa da kasa bisa tushen kundin tsarin mulkin MDD.(Murtala Zhang)