logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya yabawa Sin game da tallafin kaso na biyu na riga-kafin COVID-19

2021-02-26 09:43:55 CRI

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, a jiya Alhamis ya godewa kasar Sin sakamakon samarwa kasar Zimbabwe kashi na biyu na gudunmawar riga-kafin annobar COVID-19.

Mnangagwa ya bayyana cewa, a ranar Laraba ne aka sanar da shi cewa an sake kaiwa kasarsa gudunmawar riga-kafi kimanin 200,000 daga shugaban kasar Sin Xi Jinping a madadin gwamnatin Sin da al’ummar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda kawo yanzu a jimlace kasar Sin ta baiwa Zimbabwe gudunmawar riga-kafi COVID-19 guda 400,000.

Ya ce a madadin gwamnatin kasarsa da jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF da kuma al’ummar kasar Zimbabwe, suna godewa jama’ar kasar Sin bisa wannan karanci da suka yi musu.

Shugaban ya kara da cewa, baya ga gudunmawar, kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin zai sayarwa Zimbabwe karin wasu alluran riga-kafin kimanin miliyan 1.8.

A kalla alluran riga-kafin COVID-19 guda 600,000 daga cikin miliyan 1.8 na kamfanin Sinopharm ake sa ran zai isa kasar ta Zimbabwe a farkon watan Maris.(Ahmad)