logo

HAUSA

Jam’iyya mai mulki a Zimbabwe ta yi kakkausar suka ga ‘yan siyasar yammacin duniya saboda kirkirar karya da ta shafi Xinjiang

2021-03-24 10:54:03 cri

Sakataren kula da huldar diplomasiyya na jam’iyyar mai rike da mulki a Zimbabwe wato “African National Union-Patriotic Front” ko (ZANUPF) Mr. Simbarashe Mumbengegwi, ya rubuta sharhi a kwanan baya a jaridar The Herald ta kasar, inda ya karyata, tare da yin kakkausar suka kan karairayin da wasu ‘yan siyasar kasashen yamma suka yi, ciki har da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, na cewa wai kasar Sin ta yi kisan kare-dangi a jihar Xinjiang.

Sharhin ya ce, gwamnatin kasar Sin ta bude kofa da nuna gaskiya game da batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang, kuma ta gayyaci jami'an diflomasiyya, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da 'yan jaridu da shugabannin addinai da dama don su ziyarci Xinjiang.

Wakilin jam’iyyar ZANUPF din wanda ya taba ziyartar jihar ta Xinjiang bisa gayyatar da aka yi masa, ya ce ya ganewa idanun sa irin nasarorin da aka samu sakamakon manufofin da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar a jihar, da ma alfanun da gwamnatin kasar ta samar wa jama'ar kabilu daban daban da ke Xinjiang. (Bilkisu)