logo

HAUSA

An fara bayar da allurar riga kafin COVID-19 a Zimbabwe

2021-02-19 10:43:18 CRI

An fara bayar da allurar riga kafin COVID-19 a Zimbabwe_fororder_1127112356_16136821641971n

Gwamnatin Zimbabwe, ta ce ta fara shirinta na bayar da allurar riga kafin COVID-19, biyo bayan isar kashin farko na alluran kamfanin Sinopharm da kasar Sin ta ba ta da gudummuwarsu.

A ranar Litinin da ta gabata ne, kasar Zimbabwe ta karbi alluran riga kafi 200,000 daga kasar Sin.

Mataimakin shugaban kasar kuma ministan lafiya, Constantino Chiwenga shi ne mutum na farko da ya karbi allurar ta kamfanin Sinopharm, lamarin da ya kaddamar da aikin dake da niyyar yi wa akalla al’ummar kasar miliyan 10 daga cikin jimilarsu ta miliyan 16 riga kafi.

Da yake jawabi bayan karbar allurar, Constantino Chiwenga ya bukaci al’ummar kasar su kasance masu kwarin gwiwa kan riga kafin

Ya ce ma’aikatarsa ta gudanar da dukkan wasu binciken kimiyya da ake bukata na tantance nagartar allurar riga kafin ta Sinopharm, wadda ingancinta ya kai kaso 79.

Ya ce ya karbi allurar tare da mataimakinsa da ma’aikata, a don haka yake kira ga jama’ar kasar su karbi allurar a cibiyar lafiya mafi kusa da su.

Zimbabwe ta sayi allurai 600,000 na kamfanin Sinopharm daga kasar Sin, inda ake sa ran za su isa kasar a cikin watan Maris.

Zuwa yanzu, mutane 35,423 ne aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Zimbabwe, yayin da 1,418 suka mutu sanadiyyarta. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha