logo

HAUSA

Rukunin karshe na jiragen ruwan dake zaman tirshan sun tsallaka mashigin ruwan Suez Canal

2021-04-04 17:11:01 CRI

Wani jami’i ya sanar da cewa a ranar Asabar ne ake sa ran rukunin karshe na jiragen ruwan dake zaman tirshan a sakamakon kafewar da makeken jirgin ruwan dakon kayan nan da ake kira Ever Given ya yi a kan hanyar mashigin ruwan Suez Canal.

Cikin wata sanarwa, shugaban hukumar kula da mashigin ruwan Suez Canal (SCA), Osama Rabie, ya bayyana cewa, ana sa ran wucewar ragowar jiragen ruwan kimanin 61, da kuma karin wasu sabbin jiragen ruwan dakon kayan guda 24, a ranar Asabar.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyuka domin tabbatar da ganin dukkan jiragen ruwan dake zaman tirshan sun tsallake mashigin ruwan Suez Canal.

A ranar 23 ga watan Maris ne, katafaren jirgin ruwan dakon kayan mai tsawon mita 400 da fadin mita 59 ya makale a muhimmiyar hanyar mashigin ruwan bayan da ya saki hanyarsa sakamakon kadawar iska mai karfi da guguwa.

Lamarin ya haifar da tsayar da sufurin jiragen ruwa har na tsawon kwanaki shida, lamarin da ya haddasa dakatar da jiragen ruwa kimanin 422.

Mashigin ruwan Suez Canal wanda ya hada tekun bahar Rum da tekun maliya, wata muhimmiyar hanya ce a fannin harkokin sufurin jiragen ruwa na duniya tun bayan amincewar da aka yi ga jiragen ruwa su yi zirga-zirga tsakanin kasashen Turai da kudancin Asiya ba tare da ratsawa ta yankin Afrika ba, wanda hakan ya rage tsawon tafiya a tsakanin Turai da Indiya da kusan kilomita 7,000.

Kusan kaso 12 bisa 100 na dukkan kasuwancin duniya yana gudana ne ta hanyar mashigin ruwan Suez Canal.(Ahmad)

Ahmad