logo

HAUSA

Tekun Suez Canal na Masar zai nemi diyyar sama da dala biliyan guda saboda hasarar da aka tafka a sanadin makalewar makeken jirgin ruwa

2021-04-02 10:34:07 CRI

Tekun Suez Canal na Masar zai nemi diyyar sama da dala biliyan guda saboda hasarar da aka tafka a sanadin makalewar makeken jirgin ruwa_fororder_210402-Suez Canal

Hukumar dake kula da tekun Suez Canal ta kasar Masar SCA, za ta nemi a biya diyyar sama da dala biliyan 1 sakamakon hasarar da aka tafka wanda makeken jirgin ruwan dakon kayan nan mai suna EverGreen ya haifar bayan da ya makale ya kuma toshe hanyar jiragen ruwan har na tsawon kwanaki shida, shugaban hukumar ta SCA Osama Rabie, ya bayyana hakan.

A hirar da ya yi da gidan talabijin na kasar a ranar Laraba, Rabie ya bayyana cewa, za a biya diyyar ne sakamakon hasara da kuma barnar da aka samu, wanda zai iya zarce na dala biliyan guda. Ya ce wannan hakki ne na kasar kuma ba za su taba yin kasa a gwiwa ba.

Makeken jirgin ruwan wanda ke da karfin daukar nauyin da ya kai ton 224,000 ya kafe ne a muhimmiyar hanyar tekun Suez a ranar 23 ga watan Maris kuma an yi nasarar janye shi bayan kwanaki shida bisa ayyukan ceto na hadin gwiwa tsakanin hukumar SCA, da kamfanin Boskalis na kasar Netherland, da kuma tawagar ayyukan gaggawa ta SMIT wanda mamallakin jirgin ruwan na EverGreen ya dauko hayarsu.

Shugaban hukumar SCA ya bayyana cewa diyyar da hukumar ke nema ba kawai saboda hasarar kudaden da kafewar jirgin ya haifar na tsawon kwanaki shida ba ne, har ma ya hada da kudaden da za a biya masu aikin yashe tekun da kuma hasarorin da aka samu a lokacin aikin ceto domin janye jirgin ruwan. (Ahmad)