logo

HAUSA

Masar na murnar cika shekaru 150 da bude mashigin Suez domin zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin kasa da kasa

2019-11-18 12:00:22 cri

Hukumar kula da harkokin mashigin Suez ta Masar SCA, ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 150 da bude mashigin ga zirga zirgar jiragen ruwa tsakanin kasa da kasa.

Da yake jawabi yayin bikin murnar da ya gudana a harabar hukumar SCA dake lardin Ismailia, shugaban hukumar, Osama Rabie, ya yi alfahari da irin rawar da Mashigin Suez ya taka tun bayan kaddamar da shi a shekarar 1869 zuwa yanzu, wajen hidimtawa harkokin cinikayya na duniya da raya bangaren fiton kayayyaki ta ruwa.

Mashigin Suez hanyar sufuri ne ta ruwa mai sigar teku da aka gina a Masar, wanda ke hada tekun Bahar Rum da Bahar Maliya. Kuma an bude shi ne ga zirga-zirgar jiragen ruwa a watan Nuwamban 1869, bayan da aka shafe shekaru 10 ana gina shi.

Mashigin Suez na daya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya, la'akari da yadda take bada damar zirga-zirga tsakanin Turai da Kudancin Asia ba tare da zagaye nahiyar Afrika ba, wanda kuma ya rage nisan tafiya tsakanin Turai da Indiya da kimanin kilomita 7,000.

A shekarar 2015, Masar ta bude sabuwar hanyar ruwa mai kilomita 35 baya ga mishigin Suez mai kilomita 190, tare da fadadawa da zurfafa wani bangare na mishigin Suez da Kilomita 37.

An tsara sabuwar hanyar da aka samar, wadda wani bangare ne na gagarumin aikin fadada tashar Suez da kayayyakin fito da gina babban yankin masana'antu, domin daukaka darajar Masar a duniya da kuma mayar da kasar babbar cibiyar cinikayya.

Shugaban na hukumar SCA, ya ce tun bayan kaddamar da Mashigin Suez, jiragen ruwa miliyan 1.3 ne suka bi hanyar mashigin, dauke da kayayyakin da nauyinsu ya kai ton biliyon 28.6, inda kuma suka samar da kudin shigar da ya kai dala biliyan 135.9 ga kasar. (Fa'izaMustapha)