logo

HAUSA

Ana sa ran maido da zirga-zirga a mashigin ruwa na Suez nan da kwanaki 4 masu zuwa

2021-03-30 14:05:45 CRI

Jiya Litinin 29 ga wata, Osama Rabie, shugaban hukumar kula da harkokin mashigin ruwa na Suez ta kasar Masar ya ce, ana sa ran maido da zirga-zirga a mashigin ruwan nan da kwanaki 4 masu zuwa.

A yayin taron manema labaru da aka yi a birnin Ismailia da ke arewa maso gabashin kasar, Rabie ya bayyana cewa, jiragen ruwa sun fara tafiya a mashigin ruwan Suez tun daga karfe 6 na yammacin ranar 29 ga wata, bayan da wani babban jirgin dakon kaya ya toshe hanyar na wasu kwanaki. Kafin tsakar ranar 30 ga wata jiragen ruwa 113 sun ratsa ta mashigin ruwan. Hukumar za ta ci gaba da daidaita matsalar cuncuson jiragen ruwa, ana kuma sa ran maido da zirga-zirgar jiragen ruwa baki daya a mashigin ruwan nan da kwanaki 4 masu zuwa. 

A ranar 23 ga wata, wani babban jirgin ruwan dakon kaya mai tutar kasar Panama ya malake a mashigin ruwan Suez, inda ya toshe hanyar mashigin ruwan baki daya. Bayan da aka shafe wasu kwanaki ana ayyukan ceto, an yi nasarar fitar da jirgin ruwan dakon kayan daga wurin da ya malake a ranar 29 ga wata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan