logo

HAUSA

Manyan jiragen ruwan dakon kaya kusan 321 sun mamaye ruwan tekun Suez Canal yayin da ake aikin ceto babban jirgin ruwan da ya makale

2021-03-28 17:18:21 CRI

A kalla manyan jiragen ruwan dakon kaya kusan 321 ne suka mamaye mashigar teku Suez Canal ta kasar Masar yayin da suke zaman jiran aikin ceto babban jirgin ruwan dakon kaya na Ever Given wanda ya makale, kana ya toshe hanyar jiragen ruwan a tekun tun a ranar Talata, Osama Rabie, shugaban hukumar kula da tekun Suez Canal (SCA) ya sanar da hakan.

Osama Rabie ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai jiragen aikin ceto kimanin 14 dake kokarin ceto makeken jirgin ruwan na Ever Given daga dukkan kusurwoyi.

Makeken jirgin wanda ke da karfin daukar nauyin da ya kai ton 224,000, ya makale ne a ranar Talatar da ta gabata akan hanyar ruwan tekun bayan kauce hanyarsa sakamakon iska mai karfin gaske da ma guguwa mai hade da rairayi, lamarin da ya sa hukumar ta SCA ta sanar da dakatar da ayyukan sufurin tekun na wucin gadi.

Rabie yace, za a gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin hadarin bayan kammala aikin ceton.

Tekun Suez Canal, wanda ya hada Bahar Rum da tekun maliya wato Red Sea, ya kasance kashin bayan harkokin sufurin teku na kasa da kasa tun bayan da aka amincewa jiragen ruwa su gudanar da zirga-zirga tsakanin kasashen Turai da kudancin Asiya ba tare da ratsa sassan Afirka ba, lamarin da ya rage nisan tafiya tsakanin kasashen Turai da Indiya da kusan kilomita 7,000.(Ahmad)