logo

HAUSA

Sin na samarwa kasashe 80 da kungiyoyin kasa da kasa 3 tallafin rigakafin COVID-19

2021-03-30 21:42:06 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin na samarwa kasashe 80, da kungiyoyin kasa da kasa 3 tallafin rigakafin COVID-19. Kaza lika Sin na samarwa sama da kasashe 40 rigakafin, tana kuma hadin gwiwa da karin wasu kasashen sama da 10, a fannin binciken rigakafi, da samarwa da kuma sarrafa shi.

Hua Chunying ta yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na yau Talata, bayan da a jiya Litinin, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewa, akwai wagegen gibi a fannin gudanar da rigakafi tsakanin kasashe mawadata, da wanda ake baiwa kasashe masu karamin karfi karkashin shirin COVAX.

Jami’ar ta kara da cewa, rigakafi muhimmin makami ne na yaki da cutar COVID-19, wanda zai taimaka matuka wajen ceto rayukan al’umma, don haka ya kamata a raba shi ga dukkanin sassan duniya, ta yadda bil adama zai amfana da shi.

Daga nan sai ta bayyana kwazon kasar Sin, na shigewa gaba wajen samar da rigakafin ga dukkanin duniya, ta yadda ya zama wata hajar duniya kamar yadda ta alkawarta, yayin da kuma take kara azamar kyautata samuwarsa a farashi mai rahusa ga kasashe masu tasowa.

A daya hannun kuma, Sin ta amsa kiran MDD game da samar da gudummawar rigakafi ga jami’an wanzar da zaman lafiya na sassan duniya daban daban. Hua Ta ce "A shirye muke mu yi hadin gwiwa, da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa wajen samar da rigakafi ga ‘yan wasa, dake shirin shiga a fafata da su yayin gasar wasannin Olympic dake tafe."   (Saminu)