logo

HAUSA

Gudummawar rigakafin COVID-19 na Sin ya isa Habasha

2021-03-30 20:40:26 CRI

A yau Talata ne wani kaso na gudummawar alluran rigakafin da Sin ta samar wa kasar Habasha ya isa kasar. Rigakafin na kamfanin Sinopharm ya isa filin jirgin saman Bole na birin Addis Ababa fadar mulkin kasar, inda ya samu tarba daga jakadan kasar Sin a Habasha Zhao Zhiyuan, da ministar lafiyar kasar Lia Tadesse, da kuma karamin ministan harkokin wajen kasar Birtukan Ayano.

Da yake tsokaci ga manema labarai game da hakan, jakada Zhao ya ce "Sin ita ce kasar farko da ta samarwa Habasha gudummawar rigakafin COVID-19, karkashin tanadin hadin kan kasashen biyu, wanda hakan ke nuni ga irin managarcin zumuncin gargajiya dake wakana tsakanin kasashen.”

A nata bangaren, ministar lafiyar Habasha Lia Tadesse, ta jinjinawa wannan tallafi na Sin, wanda ta ce shaida ce dake jaddada alakar kut da kut dake tsakanin Sin da Habasha.

Madam. Tadesse ta kuma ce, gudummawar rigakafin na kamfanin Sinopharm, zai taimakawa shirin Habasha na yiwa kaso 20 bisa dari na daukacin al’ummar ta rigakafin wannan cuta ta COVID-19.  (Saminu)