logo

HAUSA

WHO ta fitar da rahoto game da aikin binciken gano asalin COVID-19 a duniya

2021-03-31 09:58:41 CRI

Jiya ne hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da rahoton binciken gano asalin cutar COVID-19 a duniya, biyo bayan kammala aikin binciken hadin gwiwa da ta gudanar da kasar Sin, kan wasu batutuwa, ciki har da hanyoyin da kwayar cutar take bi da makomar binciken a sauran kasashe.

Baki daya dai, masana 34 daga WHO da kasar Sin ne, suka gudanar da wani binciken hadin gwiwa na kwanaki 28, daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu a birnin Wuhan na kasar Sin. Yayin aikin binciken, masanan sun mayar da hankali ne, wajen gano yiwuwar hanyar da cutar ta bi har ta bulla. A cewar rahoton, bullar COVID-19 ta wata hanyar wani abu mai rai, “abu ne da ake ganin yiwuwarsa”. Sannan bullar cutar ta hanyar daskararren abinci “na iya yiwuwa”, kana bullar cutar bisa kuskure daga dakin bincike, “akwai shakku kan aukuwarsa.”

Haka kuma, masanan sun gabatar da jerin shawarwari game da gudanar da bincike a nan gaba: yadda za a tsara cikakken rumbun adana muhimman bayanai, da gudanar da karin bincike kan cututtuka cikin sauri da wuraren da ake ganin sun bulla, da yin sharhi kan irin rawar da wuraren adana daskarren abinci ke takawa kan yiwuwar bulla da yaduwar kwayar cuta.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasarta ta yi imanin cewa, binciken hadin gwiwar, zai taka gagarumar rawa wajen yayata hadin gwiwar kasa da kasa wajen gano asalin COVID-19. (Ibrahim)