logo

HAUSA

Daraktar cibiyar CDC ta Amurka ta yi gargadi game da yiwuwar kazantar yanayin bazuwar Covid-19

2021-03-30 21:52:23 CRI

Labarin da muka samu daga kafar CNN ta Amurka na cewa kasar ta gamu da koma baya, a yakin da take yi da cutar COVID-19, sakamakon yadda cutar take kara bazuwa a baya bayan nan a jahohi da dama na kasar.

Game da hakan, daraktar cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta kasar Dr. Rochelle Walensky ta bayyana cewa, tana da fargaba game da abun da ka iya faruwa nan gaba.

Ta ce “Abun da muka gani cikin makon da ya gabata, na nuni ga karuwar masu harbuwa da cutar”.

Ta ce "Na lura yanayin yana karuwa, ina kuma fargabar yiwuwar kara barkewarta kamar yadda muka samu a lokacin zafi da ma lokacin hunturu da suka wuce." (Saminu)