Rigakafin COVID-19 Na Kasar Sin Yana Kare Mutane Har Fiye Da Rabin Shekara
2021-03-29 10:45:22 CRI
Yanzu haka kasar Sin tana gaggauta yi wa al’ummarta allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa tsarin da ta tsara yadda ya kamata. Yawan alluran da aka yi amfani da su ya wuce miliyan 100 a duk fadin kasar. Wang Huaqing, babban mai tsara shirin yin alluran rigakafin cuta na cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar Sin ya bayyana jiya Lahadi cewa, rigakafin kasar Sin yana kare mutane har fiye da watanni 6 baki daya.
A yayin taron manema labaru, Wang Huaqing ya yi karin bayani cewa, yanzu mutanen da aka yi musu alluran suna da kariyar cutar COVID-19 har fiye da watanni 6. Amma ingancin alluran bai dogara da kariyar cutar ita kadai ba. Don haka akwai bukatar ci gaba da nazari kan tsawon lokacin da rigakafin zai dauka wajen kare mutane.
Zhang Yuntao, mataimakin shugaban kamfanin nazarin halittu na kasar Sin na kamfanin SINOPHARM ya yi bayani cewa, kamfaninsa ya tsara shirin samar da wata allura ta daban don kyautata amfanin rigakafin na kare mutane, zai kuma fara yi wa mutane alluran a kasashen ketare. A cewar, mista Zhang, sakamakon nazari ya nuna cewa, alluran za su kara taimakawa wajen tsawaita lokacin kare mutane daga kamuwa da cutar ta COVID-19 da kuma yaki da annobar yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Rigakafin Sinopharm da kasar Sin ta bada gudunmawarsu sun isa Sudan
- Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa
- Sin: An yiwa mutane sama da miliyan 80 rigakafin COVID-19
- An yiwa mutane sama da miliyan 100 allurar rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin