logo

HAUSA

Sin: An yiwa mutane sama da miliyan 80 rigakafin COVID-19

2021-03-25 09:54:18 CRI

Kwamitin “ko ta kwana” game da yaki da cutar COVID-19 na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya ce ya zuwa yanzu, an yiwa mutane sama da miliyan 80 rigakafin cutar COVID-19 a sassan kasar Sin daban daban.

Kwamitin ya kuma ce a mataki na gaba kuma, Sin ta tsara gaggauta yin rigakafin, wanda kyauta ne, ta yadda daga mutane masu fuskantar barazanar saurin harbuwa da cutar, aikin zai kai ga dukkanin sassan al’ummar kasar.

Da fari dai, an fara yiwa mutanen da shekarun haihuwar su ya haura 60 ne rigakafin a wasu yankuna, amma a halin yanzu za a gaggauta fadada aiki. Kaza lika za a samar da rabutattun sakwanni game da tasirin rigakafin, musamman ga wadanda ke fama da cututtuka, kamar hawan jini da ciwon suga.

Kwamitin na “ko ta kwana” ya kara da cewa, adadin allurar rigakafin COVID-19 da aka samar a ko wace rana a kasar Sin, ya karu daga kimanin miliyan 1.5 a watan Fabarairu, zuwa miliyan 5 a yanzu haka. (Saminu)