logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa

2021-03-25 10:49:49 CRI

A jiya Laraba 24 ga wata ne ka ayiwa shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, wadda kamfanin kasar Sin ya hada, kuma jin kadan bayan yi masa rigakafin, shugaba Mnangagwa ya jinjinawa goyon baya da tallafin da kasar Sin take baiwa kasarsa, yayin da take kokarin shawo kan wannan annoba, ya kuma yi kira ga al’ummun kasarsa, da su yi allurar a kan lokaci, domin ingiza farfadowar tattalin arziki da sana’ar yawon shakatawa a kasar.

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa_fororder_1.JPG

A yammacin jiya Laraba, aka yi wa shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa allurar rigakafin cutar COVID-19 ta Sinovac, wadda kamfanin kasar Sin ya hada, a wani asibitin gwamnatin dake birnin Victoria Falls, birnin da ya yi suna a fannin sana’ar yawon shakatawa, bayan kuma yi masa rigakafin, shugaban ya sanar da cewa, "Na riga na karbi allurar rigakafin cutar COVID-19, a nan ina sanar da cewa, an kaddamar da mataki na biyu na aikin allurar rigakafin a fadin kasar Zimbabwe a hukumance.”

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sayi allurar rigakafin Sinovac ne daga kasar Sin, kuma an kawo allurar ne tare da rukuni na biyu, na allurar rigakafin da gwamnatin kasar Sin ta samar wa Zimbabwe kyauta, a ranar 16 ga watan Maris da muke ciki.

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa_fororder_2.JPG

Shugaba Mnangagwa ya ce, rigakafin ba ta da wani zafi ko kadan, kuma ba ta sanya rashin lafiya, kana ya sake godewa kasar Sin a wurin, saboda goyon bayan da ta samar wa kasarsa wajen kandagarkin annobar, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana samar da allurar rigakafin ga al’ummun duniya, lamarin da ya sa kasashe masu tasowa ciki har da kasarsa suka samu cin gajiya, yana mai cewa, “Ina son in sake godewa kasar Sin a nan, saboda tallafin da ta samar mana yayin kandagarkin annobar COCID-19. Zimbabwe ta samu allurar rigakafin, kuma ta ceto karin rayukan al’ummun kasar sakamakon goyon bayan kasar Sin.”

Mnangagwa ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa ya yi allurar rigakafin a birnin Victoria Falls, shi ne kira ga al’ummun kasarsa, da su yi allurar a kan lokaci, ta yadda za su shawo kan yaduwar annobar cikin sauri, tare kuma da ingiza farfadowar sana’o’i daban daban, ciki har da sana’ar yawon shakatawa a kasar. A cewarsa:“Mun sanar da mataki na biyu na aikin gudanar da allurar rigakafin COVID-19 a birnin Victoria Falls ne, domin nuna aniyar gwamnatin kasarmu ta sa kaimi kan farfadowar tattalin arziki. Gwamnatin mu tana karfafa wa mazauna birnin gwiwar karbar allurar, ta yadda za su iya karbar masu yawon shakatawa da za su zo daga sassa daban daban dake fadin duniya.”

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa_fororder_3.JPG

Tun daga watan Maris na bara, gwamnatin kasar Zimbabwe ta dauki matakin kulle, domin hana yaduwar annobar, inda aka rufe kan iyakar kasar, aka kuma soke zirga-zirgar jiragen sama. Haka kuma an hana tafiye-tafiya tsakanin biranen kasar.

Mukadashin babban shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Givemore Chidzidzi, ya bayyana cewa, an dakatar da shiga otel otel dake birnin Victoria Falls, wanda hakan ya jefa birnin cikin mawuyacin yanayin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, saboda yawancin mazauna birnin suna dogaro ne ga sana’ar yawon shakatawa, a don haka tun daga ranar 22 ga wata, gwamnatin kasar ta fara yi wa mazauna birnin allurar rigakafin. Mr. Chidzidzi yana ganin cewa, matakin gudanar da rigakafin zai taimakawa birnin fita da yanayin da yake ciki, har ya kai ga cimma burin farfado da sana’ar yawon shakatawa yadda ya kamata, yana mai cewa, “Birnin Victoria Falls, birni ne na yawon shakatawa. Ci gaban tattalin arzikin birnin ya dogara ne ga zuwan masu yawon shakatawa daga sassa daban daban na fadin duniya. Ko shakka babu, masu yawon shakatawa suna fatan zuwa yawon bude ido a wurare masu tsaro. Yanzu haka an riga an fara yi wa mazauna birnin allurar rigakafin.”

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin, bisa gudummawar rigakafin COVID-19 da take samarwa kasashe masu tasowa_fororder_4.JPG

Arnold Sibanda, direban tasi ne a birnin, ya kuma bayyana cewa, tun daga karshen watan Janairun bana, har zuwa yanzu, kusan babu masu yawon shakatawa da suka zo wurin bude ido, kuma a cikin watanni biyu da suka gabata, ya samu aiki sau hudu ne kacal, a don haka yana fatan mazauna birnin za su je yin allurar rigakafin a kan lokaci, saboda hakan zai farfado da birnin cikin sauri, yana mai cewa, “Kowanenmu ya gamu da matsala sakamakon yaduwar annobar COVID-19, shi ya sa na amince cewa, dabara daya kacal da ta dace ita ce yin allurar rigakafin.”(Jamila)