logo

HAUSA

Rigakafin Sinopharm da kasar Sin ta bada gudunmawarsu sun isa Sudan

2021-03-27 15:53:15 CRI

Rigakafin Sinopharm da kasar Sin ta bada gudunmawarsu sun isa Sudan_fororder_210327-Sudan

Rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm da kasar Sin ta bada gudunmawarsu ga Sudan, sun isa kasar a jiya Juma’a.

Jakadan Sin a Sudan Ma Xinmin da shugaban kwamitin koli kan ayyukan lafiya na gaggawa na kasar, Saddiq Tawer da ministan lafiya na kasar Omer Al-Najeeb ne suka karbi riga kafin a filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Khartoum.

Ma Xinmin, ya shaidawa manema labarai a filin jirgin saman cewa, kasar Sin ta samar da riga kafin ne domin taimakawa Sudan yaki da COVID-19. Kana alama ce dake nuna abota da dangantaka mai karfi dake tsakanin kasashen biyu da jama’arsu.

A nasa bangaren, ministan lafiya na kasar, Omer Al-Najeeb, ya yabawa taimakon da Sin ke ba Sudan, yana mai cewa, ba kadai a lokacin annobar kasar Sin ta taimakawa kasar ba, ta kuma taimaka wajen gina cibiyoyin lafiya a Khartoum da sauran biranen kasar.

Bugu da kari, ma’aikatar tsaro ta kasar Sin, ta sanar da cewa, bisa bukatar rundunar sojin Sudan, rundunar ’yantar da al’ummar Sinawa ta PLA, ta mika mata tallafin riga kafin COVID-19

Rigakafin Sinopharm da kasar Sin ta bada gudunmawarsu sun isa Sudan_fororder_210327-Congo

Wannan na zuwa ne, kwana guda bayan rundunar ta PLA ta samar da taimakon riga kafin COVID-19 ga rundunar sojin Saliyo.

Ko a ranar Alhamis, rundunar ta PLA ta mika tallafin riga kafin ga rundunonin sojin kasashen Jamhuriyar Congo da Equatorial Guinea da Tunisia.

Wannan shi ne tallafin riga kafin COVID-19 na farko da rundunar sojin kasar Sin ta ba takwarorinta na Afrika. (Fa’iza Mustapha)