logo

HAUSA

An yiwa mutane sama da miliyan 100 allurar rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin

2021-03-23 17:43:03 CRI

A yau Talata, ofishin kandagarki da shawo kan yaduwar cutar COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ba da labari cewa, ya zuwa yanzu, an yiwa mutane allurar rigakafin COVID-19 na kasar Sin fiye da miliyan 100 a kasashe daban daban, inda dukkan alamun suka nuna cewa, allurar na da inganci, gami da amfani a fannin kare lafiyar jama’a. Kana kasar Sin ta dau niyyar samar da karin rigakafin cutar COVID-19, da kokarin yin allurar rigakafin ga daukacin al’ummar kasar, ta yadda za a samu tabbaci a fannin magance yaduwar cutar. (Bello Wang)

Bello