logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Kan Turai Ne Bisa Yanayi Na Yi Min In Maka

2021-03-24 14:21:28 CRI

Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Kan Turai Ne Bisa Yanayi Na Yi Min In Maka_fororder_sin

Ranar 22 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da sanya takunkumi kan mutane 10 da hukumomi ko kungiyoyi guda 4, wadanda suka gurgunta ikon mulkin kanta da moriyarta, da yada karya da labaran bogi da mugun nufi. Sin ta mayar da martanin ne bisa yanayi na “yi min in maka”. Lamarin ya nuna karfin zuciyar Sin, da aniyyarta wajen kiyaye ikon mulkin kasa, da tsaronta, da ci gabanta.

Hakika dai kafin bangaren Turai ya yi shelar sanya wa kasar Sin takunkumi bisa hujjar batun hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, kasar Sin ta bayyana karara cewa, tabbas za ta mayar da martani. Kuma yanzu kasar Sin ta cika wannan alkawari na ta.

Wadanda kasar Sin ta sanar da sanyawa takunkumin dai sun bata sunan al’ummar kasar Sin da mutuncinsu, sun gurgunta ikon mulkin kasar Sin da tsaron kasar. Kasar Sin ta sanya takunkumin kansu ne daidai da abubuwan da suka aikata.

Alal misali, Adrian Zenz ko kuma Zheng Guoen da aka fi san sa da shi, ya bayyana kansa wani masani a kasar Jamus, ya yi karairayi kan jihar ta Xinjiang. Bai taba zuwa Xinjiang ba, amma ya rubuta bayanai da rahotanni fiye da 10 ne a kan jihar tun daga shekarar 2018, bisa tunaninsa da kuma zatonsa kawai.

Ya dora wa kasar Sin laifin wai kisan kare dangi da dai sauransu. Amma a shekaru fiye da 40 da suka wuce, yawan ‘yan kabilar Uygur a jihar ta Xinjiang ya haura zuwa miliyan 12 da dubu 700, daga miliyan 5 da dubu 550, kana matsakaicin tsawon rayukan mutane ya wuce shekaru 72 daga 30 da haihuwa. Yadda Zheng Guoen ya shafa wa kasar Sin kashin kaji, ya nuna ainihin mugun nufinsa, a matsayin kusar hukumar nuna kiyayya ga kasar Sin.

Amma karyar da ya yi ta samu goyon bayan wasu ‘yan siyasan kasashen yammacin duniya, wadanda suke kin jinin kasar Sin. Ba su lura da hakikanin abubuwa ba, ba su kuma kula da hakkin al’ummar Xinjiang ba. Ba sa son ganin ci gaban kasar Sin, da yadda mutanen Sin suke jin dadin zamansu. Wadannan ‘yan siyasa sun yada karyar Zheng Guoen, a yunkurin cimma burinsu na hana ci gaban kasar Sin, bisa hujjar batun Xinjiang.

An lura da cewa, bayan da kungiyar tarayyar Turai ta yi shelar sanyawa kasar Sin takunkumi bisa hujjar batun hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, kasashen Amurka da Birtaniya su ma sun dauki matakai, sun hada hannu wajen sanyawa kasar Sin takunkumi bisa hujjar “kiyaye hakkin dan Adam”, da karya da kuma bayanan bogi, a yunkurin bata sunan kasar Sin da hana ci gaban kasar.

Hayaniyar siyasa ba za ta rufewa duniya idanu ba. Maxime Vivas, wani marubucin kasar Faransa ya rubuta wani littafi mai suna “kawo karshen tattara labaran bogi kan kabilar Uygur”, inda wasu jami’an kasashen duniya da ‘yan jarida, wadanda suka taba ziyartar Xinjiang suka bayyana ra’ayoyinsu kan Xinjiang. Haka kuma kwanan baya kasashe fiye da 80, sun nuna goyon bayansu ga manufar kasar Sin ta tafiyar da harkokin Xinjiang, a yayin taron kwamitin harkokin hakkin dan Adam na MDD, lamarin da ya nuna cewa, zukatan mutane sun fi amincewa da adalci. Kasashen yammacin duniya kalilan ba za su iya sarrafa zukatan kasashen duniya ba, za kuma su tono munafuncinsu, da fuska biyu da suke yi kan hakkin dan Adam.

A gaskiya dai, kasashen duniya sun fi son sanin yadda wadannan kasashen yammacin duniya da suke yin shelar kiyaye hakkin dan Adam, za su biya hasarorin da suka haddasa wajen keta hakkin dan Adam.

‘Yan mulkin mallaka daga kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa sun shafe shekaru 400 suna yin cinikin bayi. Ya zuwa yanzu mutanen kasashen ‘yan asalin Afirka suna fama da matsalar nuna bambancin launin fata a kasashen Amurka da Birtaniya. Yaya wadannan kasashen yammacin duniya suka cancanci zama malaman koyar da kiyaye hakkin dan Adam?

Babu wata hanya daya kacal da ta cancanci ko wacce kasa a duniya ta bi wajen kiyaye hakkin dan Adam. Ya fi kyau kasashen yammacin duniya su daidaita batutuwansu na kiyaye hakkin dan Adam, a maimakon nuna munafunci da fuska biyu, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata kasa ta daban, da ci gaba da bin hanya maras bullewa. In ba haka ba, kasar Sin za ta ci gaba da mayar da martani.

Wadannan malaman koyar da kiyaye hakkin dan Adam, za su girbi mummunan sakamakon aiki da suka yi. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan